Plasings

Tarihin Umar M. Shareef

Prent
Tarihin Umar M. Shareef: Daga Farkon Rayuwa Zuwa Kololuwar Nasara. Umar Muhammad Shareef, wanda aka fi sani da Umar M. Shareef, na ɗaya daga cikin fitattun mawakan Hausa da suka yi fice a masana'antar Kannywood. Ya shahara saboda murya mai daɗi, waƙoƙin soyayya masu jan hankali, da kuma fitowa a fina-finan Hausa. Haihuwa da Tasowa An haifi Umar M. Shareef a garin Rigasa da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Tun yana ƙarami ya taso cikin tarbiyyar addini da al'adun Hausawa. Kamar yawancin yara a Arewacin Najeriya, ya fara da karatun Alƙur'ani kafin ya shiga makarantar boko. Karatunsa Bayan kammala matakan karatunsa na farko da na sakandare, Umar ya ci gaba da karatu a Jami'ar Jihar Kaduna (Kaduna State University - KASU), inda ya samu ilimi mai zurfi tare da haɗa karatu da baiwar fasaha da Allah Ya yi masa. Farkon Shiga Harkar Waƙa Sha'awar waƙa ta fara bayyana a rayuwarsa tun yana matashi. Ya fara fitowa a matsayin mawaƙi a ƙarshen shekarun 2000, inda waƙoƙins...

Namijin Goro Yana Maganin Karfin Maza

Prent
  Namijin Goro, wanda ake kira Bitter Kola , yana daga cikin shahararrun tsirrai masu amfani wajen ƙara ƙarfin maza da inganta lafiyar jiki gaba ɗaya. Yadda yake aiki: Namijin goro yana taimakawa wajen ƙara yawan jini a jiki, yana ƙarfafa jijiyoyin maza, kuma yana motsa sha’awa ta hanya ta halitta. Har ila yau, yana taimaka wajen rage gajiya da saurin fitar maniyyi. Yadda ake sarrafa shi: A ɗauki namijin goro a wanke shi sosai. A niƙa shi ya zama gari ko a yayyanka ƙanana. A haɗa da zuma ta halitta da ganyen goron dutse ko dabino idan ana so a ƙara ƙarfin tasiri. A rika ɗauka ƙanana bayan cin abinci, sau biyu a rana. Gargaɗi: Kada a sha fiye da kima. A guji amfani da shi idan ana da matsalar hawan jini ko ulcer. Magani daga tsirrai, lafiya ta gaskiya ce. Kalam Waheed Herbal Medicine – Cibiyar Bada Maganin Gargajiya da Bincike Akan Tsirrai.

Fara Rijistar PVC Online – Agusta 18, 2025

Prent
INEC Ta Kaddamar da Rijista Yau 18/08/2025 A ranar Litinin, 18 ga Agusta 2025 , Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) ta sauka da sanarwar fara rajistar masu jefa kuri’a ta yanar gizo (online pre-registration) a duk fadin ƙasa ( INEC CVR Portal , Wannan ya kasance wani muhimmin mataki zuwa ga babban zaɓen 2027. Shafin da aka fara amfani da shi ne CVR portal (cvr.inecnigeria.org) wanda ya buɗe dama ga matafiya kamar haka: Sabuwar rijista (pre-registration) Sabunta bayanai (update information) Canja wurin zaɓe (transfer polling unit) Duba matsayi (status tracking) Nemo cibiyoyin rijista da wuraren ɗaukar PVC ( INEC CVR Portal ,  Matakan Yin Rijistar Online Ga matakan da za ka bi domin yin rijista ko sabunta PVC ɗinka ta yanar gizo: Ziyarci cvr.inecnigeria.org ( INEC CVR Portal ). Yi rajistar account ta email, Gmail, ko Facebook. Cika bayananka (suna, ranar haihuwa, adireshi) kuma loda hoton pasfoto. Zaɓi ranar zuwa cibiyar najwar domin ɗaukar biometrics ...

Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan adam

Prent
  Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan adam Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper. ‘yayan kankana wadan da ake kira da ‘tarbooj ke beeja’ yaren hindi, ana amfani dasu kamar a kasar Asia, a matsayi kayan abinci, inda a Najeriya kuma ake amfani da ita a cikin miya, inda man ‘ya’yan kuma ana amfani dashi a don gyara fatar jiki. Ga wasu daga cikin amfanonin ‘ya’yan kankana a jikin dan adam: 1. ‘Ya’yan kankana suna wadatarda jikin dan adam da sinadaran magnesium wanda ke taimakawa zuciya wurin harba jinni da kuma magance ciwon diabetis. 2 .‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji. 3. ‘Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam. 4. ‘Ya’yan kankana an...

Amfanin zogale 10 a jikin dan adam

Prent
A mfanin zogale 10 a jikin dan adam Masu iya magana sunce lafiya ce uwar jiki, sannan kuma abu ne da kudi baya iya siyansa. A zamanin nan da muke ciki cuttutuka sunyi yawa inda ya zama babu babba babu yaro, hakan ne ya sa muka binciko maku wasu magani da ganyen zogale ke yi a jikin dan adam. Ga wasu daga cikin amfani 10 da zogale ke yi: 1. Da farko zaa dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin magance gyambon ciki wato ulcer. 2. Duk wanda ke fama da ciwon kai ya nemi ganyen zogale ya shafa a goshinsa. 3. Ganyen zogale na amfani wajen tsayar da jini idan mutun ya yanke. 4. Ana hada zogale da man zaitun domin maganin kurajen jiki. 5. Ana zuba garin zogale a cikin abinci ga mai cutar hawan-jini da neman karin kuzari. 6. Zogale na saurin warkar da rauni ko gyambo. 7. Fure zogale da zuma na kara wa mace ruwan nono a lokacin da take shayarwa. 8. Ana dafa furen zogale da citta domin magance ciwon siga da yawan fitsari. 9. Ga mai ciwon shawara ya nemi zogale da kanwa kadan ya dafa. 10...